Logo Lanfrica

Misbah-Engr/CourseDinblockchain

Domain:

natural language processingdigital infrastructure

Record type:

project
Creator:
Mis
Host:
Wannan shine course din Blockchain na farko da Hausa a Duniya. # Course Din Blockchain Development Wannan shine course din Blockchain Development na farko da Hausa a Duniya. ## “IDAN KA KASHE WATA UKU BAKA KOMAI SAI KOYO TARE DA JAGORANCI ZAKA IYA ZAMA BLOCKCHAIN DEVELOPER” Inji DS Central, kuma zaka iya samun aiki a cikin wata 12 na farko idan kayi da gaske. Fasahar Blockchain, ‘Mahadi ka ture’ kamar yadda Marigayi Malam Nasir Mahuta ya kira ta, ta riga ta zama ruwan dare mai game duniya. Manyan kamfanonin takanoloji na duniya irinsu Meta, Google, da Microsoft, kawai zuba hannun jari suke a Blockchain development don su fada cikin Blockchain da karfinsu. Yanzu dukkan wadannan kamfanonin ai kowa da abinda yake ginawa, amma a ina suka yi kama? Inda suka yi kama gaba dayansu shine suna bukatar blockchain developers su taya su aiki su biya su. Blockchain developer jarumin mutum ne da ya kware wajen kera softuwayan blockchain. Dukkan software developer a duniya suna yin kaifin tunani da aiki na jarumta tukuru don hada software. Shi kuma blockchain developer yana nuna bajintar sa wajen samar da cryptocurrency, smart contracts, nfts, blockchains, scaling solutions, da sauransu. ## DALILAI BIYAR DA ZASU SAKA KA ZAMA BLOCKCHAIN DEVELOPER 1. In dai ka kware, ana samun aiki da wuri saboda ana bukatar kwararrun developers 2. Za ka zama mutum mai fasaha da kirkira, mutane zasu dinga sha’awar zama irinka saboda kwazonka da fasahar ka zata karu 3. Ana samun kudade masu tsoka. Albashin su nada kauri. Manyan kwararru har dollar dubu dari uku ana biyansu a shekara. A hada smart contract guda daya kuma masu project zasu iya biyanka dollar dubu biyu ko sama da haka. Ana shiga hackathons kuma ana samun manyan kyaututtuka akan websites irin su Hackernoon, Dora Hacks, Devpost, da Techfiesta. 4. Nan gaba ba lallai ka bukaci canja sana’a ba, tunda abubuwan cigaba suke, sai dai ka kara koyon sabbin dabaru 5. Akwai mutane da yawa a fadin duniya da suke shirya su taimake ka iya komai, ka samu aiki. Kuma kai ma zaka taimaka wa communities. Watanni da yaw …