Logo Lanfrica
  • Home
  • Atlas
  • Insights
  • Docs
  • Sign in

© 2026 Lanfrica. All rights reserved. All copyrights of the resources shown on the Lanfrica website belong to the original copyright holders, unless explicitly stated otherwise.

Gurbin Adawa a Siyasar Zamani

Domain:

peace and security
Creator:
Ali
Publisher:
SAS
Host:
Salon mulkin siyasa wani tsari ne da al’umma suke zaɓen wakilansu da kansu bisa ga cancantar ɗan takara da kundin tsarin mulki ya yarda da shi. Wato, siyasa wani salon mulki ne na farar hula da ke bai wa ‘yan ƙasa ‘yanci da damar saka kansu a dama da su a sha’anin mulki. Wannan bincike mai taken Gurbin Adawa A Siyasar Zamani, bincike ne da ya shafi gudummawar da adawa take bayarwa wajen kawo sauyin salon tafiyar da shugabanci, ta hanyar haska wa masu mulki kurakuransu domin su gyara da kuma yi musu hannunka-mai-sanda ko gargaɗi ga yadda ya kamata su aiwatar da abubuwan da za su amfani al’ummar da suka zaɓe su. A wani ɓangare kuma adawa tana ilmantar da al’umma game da kyawawan ayyukan da shugabanni suka yi, ko kuma su yi ƙorafe-ƙorafe ko soke-soke a kan abubuwan da shugabanni ko ‘yan siyasa suke aikatawa waɗanda ba su dace ba. Haka kuma su jawo hankalin masu zaɓe su zaɓi mutane nagari da suka dace a lokacin jefa ƙuri’a. Hakan zai kawo gyara ga kurakuran da shugabanni suke tafkawa a lokacin da suke gudanar da mulkinsu. Haƙƙin kowane shugaba ne ya aiwatar da alƙawuran da ya yi wa al’umma a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe. Alƙawuran sukan haɗa da: Samar da ingantaccen ilimi da ruwan sha da hanyoyin sufuri da kiwon lafiya da bunƙasa aikin gona da samar da tsaro da zaman lafiya da kuma bunƙasa tattalin arziki. Rashin cika waɗannan alƙawura kan sa a sami ‘yan adawa su riƙa soke-soke da ƙorafe-ƙorafe domin su tunatar da masu mulki ko ‘yan siyasa game da alƙawurran da suka yi wa jama’a a lokacin yaƙin neman zaɓe domin su gyara. Wannan bincike zai mayarda hankali ne a kan matsayin adawa a siyasa da amfaninta da illolinta da kuma rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen kawo gyara da sauyi mai ma’ana ga yadda ake gudanar da mulkin siyasa don amfanin talakawa da ƙasa baki ɗaya.

Visit

doi.org

Languages

FangKaanKomaLokoMaasaiMbayShaThemne

Similar

Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannun Addini da ZamaniRaujin Hikima: Gurbin Waƙoƙin Gargajiya a Rayuwar HausawaGurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin BakaToniMoringa/Capstone-Zamani-AppZAMANI RIGA: BUKIN SAUKAR ALQUR'ANI A TSAKANIN AL'UMMAR HAUSAWA A QARNI NA 21Zamani, Relational SYmmetry and African Epistemology: A unique Mathematical and cognitive framework developement.

Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannun Addini da Zamani

Magani ya shafi duk wani abu da za a yi amfani da shi ko a aikata domin a samu sauƙi ko waraka daga

Raujin Hikima: Gurbin Waƙoƙin Gargajiya a Rayuwar Hausawa

Waƙoƙin Gargajiya (traditional songs) hold a significant and distinct place in Hausa culture, functi

Gurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin Baka

Wannan makala ta yi nazari a kan rayuwar Hausawa a zamantakewarsu da kazar Hausa. Tunanin wannan maƙ

ToniMoringa/Capstone-Zamani-App

ZAMANI – Kenya's Time Capsule: A retro TV-themed React app exploring global & Kenyan history via Wik

ZAMANI RIGA: BUKIN SAUKAR ALQUR'ANI A TSAKANIN AL'UMMAR HAUSAWA A QARNI NA 21

Tsakure Wannan takarda ta tattuna irin sauye-sauyen da zamani ya kawo a al’adar bukin saukar Alqur’

Zamani, Relational SYmmetry and African Epistemology: A unique Mathematical and cognitive framework developement.

This work reimagines mathematical and scientific reasoning from within a relational, embodi