Manufar wannan takarda ita ce nazartar matakan gano abin da yake ba bincike ba wanda da dama ake saka shi cikin sahun binciken ilimi. Binciken ya ginu kan salon bin ƙwaƙƙwafi tare da ƙalailaice batutuwan da ake nazarta. Rubuce-rubucen ilimi da suka gabata masu alaƙa da wannan nazari su ne suka yi matashiya tare da samar masa da bayanan da yake buƙata a matsayin majiya ko tushen bayanai na biyu. An ɗora aikin a Bahaushiyar hanyar gudanar da bincike ta “komai da mazauninsa.” Hanyar ce kuma ta samar da hasashen cewa, rashin sanya abubuwa a muhallansu ke gurɓata bincike. Binciken ya gano cewa, tasgaro a muhimman siffofin ko matakan gudanarwa na kai ga bincike ya zama ba bincike ba. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarar cewa ya kamata a samu hoɓɓasar manyan makarantu da cibiyoyin bincike da ma masana da manazarta a matsayin ɗaiɗaiku domin tabbatar da cewa waɗanda abin ya shafa na bibiyar sababbin cigaba da ake samu a fannin binciken ilimi.