Kamar yadda taken ya nuna, “Mamayar Harshe a Nijeriya: Nazari a kan harshen Karai-Karai da Huasa”
Manufar ita ce tunatarwa da jan hankali ga hukumomi da jagororin harshen kan yadda Hausa ta mamaye
harshensu. Baya ga haka, ta yi amfani da lurar gani-da-ido da rubutattun bayanai da tattaunawa da mutane
goma sha ɗaya a matsayin hanyoyin tattara bayanai domin samun ingantattun bayanai. An ɗora wannan aiki a
kan ra’in Phillipson, R.L (1992) ra’in Babakeren Harshe (Linguistic Imperialism). Haka nan, takarda ta bayyana
dalilai da suka haifar da babakeren. Daga cikin dalilai da suka haifar da babakere akwai rashin koya wa yara
harshen uwa da halin ko oho dangane da harshen uwa da tasirin addini da auratayya da wayewa ko ƙauyanci na
rashin amfani da harshen uwa da rashin koyar da harshen al’umma a makarantu da rashin amfani da harshen
wajen gudanar da taruka. Har wa yau, takarda ta bayar da shawarwari kan iyaye su riƙa koya wa yara harshensu
da amfani da harshen al’umma wajen gudanar da taruka da koyarwa a makarantu da sanya kishin harshen uwa
ga yara da sauransu. Daga ƙarshe, sakamakon bincike ya nuna Hausa ta mamaye harshen Karai-Karai da kaso
sittin (60%), Ke nan za a iya cewa harshen ya ɗauko hanyar ɓacewa wanda za ta iya kai shi ga mutuwa matuƙar
mahukunta da jagororin harshen ba su ɗauki matakan kariya da suka dace ba,