Sabon Gari Kano yanki ne da ya kasance ƙarƙashin ƙaramar hukumar Fagge da ke jihar Kano. Baƙin al’ummu su ne mazauna farko a yankin tun lokacin da hanyar jirgi ta kai garin Kano ƙarƙashin gwamnatin Turawan mulkin mallaka a shekarar 1911. Wannan takarda ta yi ƙoƙarin nazartar littafin Bako, (2006) a matsayin wani shakundum dangane da tarihin yankin musamman daga kafuwarsa zuwa ƙarni na 20. Daga nan ta yi amfani da dabarar hira domin binciko sakamakon cuɗanyar al’adu da aka samu a wanan yanki. Takardar ta yi amfani da ra’in Nashe Al’adu yayin gudanar da binciken. Sakamakon binciken ya ci karo da hasashensa, inda ya bayyana cewa, al’adun baƙin al’ummu ne suka yi tasiri a kan na Hausawa a yankin. Wato hakan ya zama koma bayan abin da aka yi hasashe na cewa al’adun Hausawa za su nashe na duk wasu al’ummu da suka tsinci kansu a yankin, kasancewar Kano ɗaya daga cikin manyan garuruwan Hausawa. Daga ƙarshe takardar ta ba da shawarwari wanda ɗaya daga ciki shi ne cewar a gudanar da nazarin da zai yi hasashen sakamakon wannan cuɗanyar al’adu ga al’ummar yankin da kuma Kano baki ɗaya.