Logo Lanfrica

Kamancin Jinsi a Sunayen Yanka na Hausawa da Wasu Harsuna (Larabci da Ingilishi)

Domaine:

natural language processing

Type de record:

paper
Créateur:
Ada
Éditeur:
Zenodo
Hôte:avatar
Daga cikin hanyoyi masu yawa da masana da manazarta suka danganta al’ummar Hausawa da Larabawa, akwai harshe, kamar yadda Greenberg (1947) da Schuh (1982) suka bayyana cewa Hausa da Larabci suna da nasaba, kasancewar, su jikoki ne na harshen Afro-Asiatic, wanda har ila yau ake kira da ‘Hamu da Sanu’, wato harshen ‘ya’yan Annabi Isma’il (A.S). Haka kuma babu harshen da ya kai Larabci daraja a wajen Bahaushe, domin shi ne harshen Alqur’ani, kuma harshen da ake koyon addinin da shi, a cewar (Zarruq 1978). Alaqar Hausawa da Larabawa ce ta sanya Hausawa aron kalmomin Larabci, baya ga haka kuma Hausawan suka koyi tsaretsarensu na gudanar da makarantun Islamiyya da shari’a da siyasa da dai sauransu, a cewar (Yalwa 1994 :4-6). Musulunci shi ne addinin da yawancin Hausawa ke bi. Saboda haka daidai ne idan aka ce, akasarin tarbiyyar Hausa ma ta wannan addini ce. A wajen musulmi, kowa yana da sunan yanka, wato sunan da aka raxa masa bayan kwana bakwai da haihuwa, A nan ne akan bai wa yaro sunayen Manzo na yabo ko sunayensa na qidaya ko sunayen danginsa da alayensa da tabi’ansa da shaihunnai da Mala’iku da sauransu. Alhassan da wasu (1982 :26-27), duk da dai a yanzu akan samu wasu Hausawan da suke raxa wa ‘ya’yansu suna a ranar da aka haife su sakamakon wasu hujjoji da suke dogaro da su, saboda qarin fahimta da ake samu a addini. A xayan vangaren kuwa, shi ma harshen Ingilishi harshe ne muhimmi, domin shi ne harshen hukuma musamman ga al’ummun da ke zaune a qasashe, rainon Ingila kamar Nijeriya da Ghana da Liberiya da Saliyo da kuma yankunan wasu qasashe rainon Faransa, kamar Nijar da Kamaru da Chadi da Ivory-Coast da dai sauransu. Abin nufi a nan shi ne, Ingilishi shi ne harshe na xaya ko na biyu da ake amfani da shi wajen gudanar da gwamnati da makarantu da kotuna da kafafen yaxa labarai da dai sauran muhimman wurare na waxannan qasashen. Har ila yau kuma, xaya ne daga cikin harsunan da Turawan Mishan (Missionaries) suka yi amfani da su wajen yaxa addinin Kirista (Christianity) a qasashen Afirka, wanda hakan ya sa mafi yawancin al’ummun da suka rungumi addinin Kirista suke sanya wa ‘ya’yansu sunaye irin na Turawa, a matsayin sunan yanka ko kuma sunan laqabi. Manufar wannan maqala ita ce fito da kamanci a cikin jinsin sunayen yanka a tsakanin al’ummar Hausawa, waxanda suka samo daga Larabawa da kuma sunayen sauran al’ummu, waxanda suka samo daga Turawa, ta hanyar amfani da xafi (affixation). Amma kafin a