Manufar wannan bincike ita ce nazartar fice da shahara da mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi a tsakanin mawaƙa a ƙasar Hausa. Domin tattara bayanai, an bibiyi ɗakunan adana bayanan ilimi, don bitar littattafai da kundaye da mujallu; musamman waɗanda suke da alaƙa da ALAn Waƙa. An ɗora aikin a kan Ra’in Tasirin Taurari a Kan Al’ada (Celebrity Theory of Culture). Ra’in ya jagoranci aikin bisa mahangar cewa, lallai ficen ALA a matsayin tauraro ya kai ya yi tasiri a al’adun Hausawa. Binciken ya gano cewa mawaƙin ya ɗamfaru da wasu siffofi nagartattu da suka zamar da shi fitacce kuma na daban a duniyar waƙa. Haka kuma, an fahimci cewa mawaƙin ya kasance tauraro da yake da nagartattun halaye da ɗabi’u da al’adu. Alaƙarsa da masu sarauta da attajirai da malamai ta sanya tauraron mawaƙin haskawa har ya zama sha-kundum kuma gagara-gasa a tsakanin takwarorinsa. Daga ƙarshe, takardar ta bayar da shawarwari da suka haɗa da kira ga yin wani gagarumin taron ƙara wa juna sani domin nazartar ɗaukacin rayuwa da waƙoƙin tauraron.
Fitattun Kalmomi: Tauraro, Ɗaukaka, Waƙa, Mawaƙa, Waƙoƙin Hausa