Logo Lanfrica

Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannun Addini da Zamani

Créateur:
SanJaj
Éditeur:
The
Hôte:avatar
Magani ya shafi duk wani abu da za a yi amfani da shi ko a aikata domin a samu sauƙi ko waraka daga wata cuta. Idan aka ce cuta kuwa a nan, za ta iya kasancewa ta ciwo ko wata damuwa ko buƙata da ta tsaya wa mutum a rai. An ɗora wannan bincike a kan ra’ayin Bahaushe na “Zamani riga.” Binciken ya mai da hankali wurin waiwaye dangane da magungunan Bahaushe na gargajiya tun daga kan hasahen samuwar asalin kalmar magani. Daga nan sai aka duba tasirin Musulunci da kuma zamani kan magungunan gargajiya na Bahaushe. Bayan haka, takardar ta nazarci amfani da koma bayan da magungunan ke tattare da su. Sakamakon na nuna cewa, ɗimbin amfanin magungunan gargajiya bai hana su samun koma baya ba. Naƙasun da suke da shi ya danganci rashin ingancin hanyar sarrafawa da adanawa da kuma amfani da magungunan. A bisa haka ne aka ba da shawarar cewa gwamnati ta samar da shiri na musamman da zai samar da horo ga masu ba da magungunan gargajiya tare kuma da ba su tallafi, duk dai don inganta sha’anin maganin gargajiyar Bahaushe.