Logo Lanfrica
  • Home
  • Atlas
  • Insights
  • Docs
  • Sign in

© 2026 Lanfrica. All rights reserved. All copyrights of the resources shown on the Lanfrica website belong to the original copyright holders, unless explicitly stated otherwise.

Kimiyyar Magungunan Ciwon Daji a Mahangar Hausawa

Domain:

healthcare

Record type:

paper
Creator:
MusDr.
Publisher:
SAS
Host:
Magani musamman na Gargajiya a wajeen Bahaushe na da matuƙar matsayi da muhimmanci ga rayuwar al’ummar ƙasar Hausa, an san Bahaushe mutum ne mai matuƙar riƙo da al’adunsa wanda ya gada tun iyaye da kakanni, barantana kan abin da ya shafi harkar magani. Maƙasudin wannan nazari shi ne fito da Magungunan ciwon daji da Hausawa suke amfani da su don kawo sauƙi da waraka a rayuwar su ta yau da kullum, sani ko fahimtar magani ya na taimakawa wajen shawo kan ciwo ko cuta da wuri kafin ta azzara a jikin majinyaci, nazarin zai yi bayani kan wasu Magungunan ciwon daji. Manufar wannan bincike kuwa shi ne ƙoƙarin fito ko tantance Magungunan Ciwon daji da Hausawa suke amfani da su don warkarwa, waɗannan magunguna ga su nan a fili ko sarari don a ƙara sanin su, ba don komi ba sai don ƙara inganta rayuwa da lafiyar Hausawa ko majinyata, musamman masu fama da ire-iren Ciwon ko cututtukan daji da suke addabar al’umma. An yi amfani ta hanyar hira, wato tattaunawa da masana magunguna da masu bayar da magani da sauran mutane a wasu ɓangarorin ƙasar Hausa da kewayanta don fito da waɗannan Magungunan ciwon daji.

Visit

doi.org

Languages

HausaKaanMasanaMbayShi

Similar

Kuɗi a mahangar karin maganaSunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu)Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannun Addini da ZamaniTasirin Musulunci a Kan Auren HausawaHausa da Hausawa a Duniyar IntanetNazarin Wasan Kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kuɗi a Mahangar Ra’in Mararanci

Kuɗi a mahangar karin magana

This research work titled ‘Kuɗi a Mahangar Karin Magana’ was a research based on Hausa Oral Literatu

Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu)

The focal point of "Sunayen Hausawa" (The Hausa Names) is an in-depth exploration of the names and n

Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannun Addini da Zamani

Magani ya shafi duk wani abu da za a yi amfani da shi ko a aikata domin a samu sauƙi ko waraka daga

Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

Rarrabe tsakanin al’adun aure da Hausawa suka gada kaka da kakanni da abubuwan da addinin Musulunci

Hausa da Hausawa a Duniyar Intanet

X.1 Matashiya Wannan littafin ya ɗauki intanet a matsayin “duniya” mai zaman kanta. A ciki (duniyar

Nazarin Wasan Kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kuɗi a Mahangar Ra’in Mararanci

Nazarin ayyukan adabin Hausa a bisa wasu ayyanannun ra’o’i abu ne da bai daɗe da bayyana a duniyar n