Logo Lanfrica
  • Home
  • Atlas
  • Insights
  • Docs
  • Sign in

© 2026 Lanfrica. All rights reserved. All copyrights of the resources shown on the Lanfrica website belong to the original copyright holders, unless explicitly stated otherwise.

Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

Creator:
HarMuh
Publisher:
SAS
Host:
Rarrabe tsakanin al’adun aure da Hausawa suka gada kaka da kakanni da abubuwan da addinin Musulunci ya ya zo da su, ba abu ne mai sauƙi ba. Idan aka lura da irin tasirin da addinin Musulunci ya yi a kusan dukkan ɓangarorin rayuwa, za a ga cewa wasu abubuwa da suka shafi aure sun sauya daga abin da al’ada ta zo da shi ya zuwa ga abin da addinin Musulunci ya zo da shi. Musulunci ya zo da dukkan tsare-tsare, kuma rashin bin wannan tsari na Musulunci, kan iya zama barazana ga auren ma’aurata da kuma rayuwarsu ta gaba ɗaya. Wannan takarda na da manufar: bayyana auren Hausawa, ta kuma fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa tare da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike ta haɗa da hira da wasu mutane da karance-karancen littattafai da kundayen binjcike. An ɗora wannan maƙalar a kan ra’in Sauyin al’adu. Maƙalar, ta fito da irin tasirin da Musulunci ya yi a wasu al’adun Hausawa na aure, tun daga kore wasu, sauya wasu, da kuma samar da wasu al’adun.

Visit

doi.org

Languages

AkaBinaHausaKaanKomaMaasaiMbayMbembe, Cross RiverShi

Similar

Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na MutuwaTasirin Finafinai a Kan Al'adun Hausawa: Keɓaɓɓen Nazari a Kan Wasu Ɗabi'u Na Musamman a Cikin Fina-Finan HausaDaga Sassabe Zuwa Lauma: Taƙaitaccen Tsokaci Game da Tasirin Zamani a Kan Abincin Hausawa

Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na Mutuwa

Manufar wannan bincike ita ce nazarin ƙwaƙƙwafi domin gano nau’ukan tasirin da addinin Musulunci ya

Tasirin Finafinai a Kan Al'adun Hausawa: Keɓaɓɓen Nazari a Kan Wasu Ɗabi'u Na Musamman a Cikin Fina-Finan Hausa

An daɗe ana amfani da wasannin kwaikwayo wajen isar da saƙwanni ga al’ummar Hausawa. Saƙwannin sun s

Daga Sassabe Zuwa Lauma: Taƙaitaccen Tsokaci Game da Tasirin Zamani a Kan Abincin Hausawa

Zamani ya zo da ƙirƙire-ƙirƙire da sauye-sauye da suka shafi abincin Bahaushe. Wannan bai taƙaita ga