About the Book
This book provides a detailed analysis of the opportunities available to the Hausa people for earning and saving within the internet economy, and it is divided into six chapters. The first chapter reviews traditional and contemporary practices of livelihood and savings among the Hausa. The second chapter focuses on traditional occupations, trade, and commerce, and examines how modernity has transformed them. The third chapter presents the history of the internet, its meaning, its development, and its impact on the Hausa people, as well as the Hausa influence on the internet. The fourth chapter explores ways of making money online, including freelance work, advertising, agency roles, and other technical and linguistic services. The fifth chapter outlines methods of saving through the internet, including keeping money in bank accounts, online wallets, and digital assets. Finally, the sixth chapter addresses strategies for effectively managing earning and saving online, covering the requirements for success (such as computer literacy and skills), as well as the benefits and challenges associated with these activities. In summary, the book shows that the internet presents a great opportunity for the Hausa people, but it requires preparation and skill to succeed in it.
Game Da Littafin
Intanet ya samu ne a shekara ta 1983, kuma tun daga lokacin ya kawo sauyi mai girma a kusan dukkanin fannonin rayuwa a duniya. Wannan sauyi ya shafi Hausa da Hausawa ta fuskoki da dama, ciki har da addini, ilimi, kiwon lafiya, shugabanci, siyasa, da tattalin arziki. Yau, duniyar intanet ta zama wata duniya ta daban wadda ke buƙatar Hausawa su sami wakilci a cikinta. Harkokin kasuwanci da biɗa da tanadi sun koma kan intanet, inda aka samu kasuwannin dijital da Hausawa suke shiga suna saye da sayarwa, har da hadahadar kuɗaɗen intanet. A gefe guda kuma, intanet ya buɗe sabbin hanyoyin ƙwadago ga Hausawa, kamar baje koli, bincike, dillanci, gyaran hotuna da na'urori, tallace-tallace, da kuma ayyukan kimiyyar harshe kamar fassara da makamantansu. Waɗannan ayyukan suna da alaƙa kai tsaye da al'ada, don haka dole ne Hausawa su shiga ciki a dama da su domin su ba da kyakkyawan wakilci ga harshe da al'adunsu.
Wannan littafi ya yi nazari dalla-dalla game da damarmakin da Hausawa suke da shi na biɗa da tanadi a duniyar intanet. An raba shi zuwa babuka shida. Babi na farko ya yi waiwaye kan harkokin biɗa da tanadi na gargajiya da na zamani na Hausawa. Babi na biyu ya mayar da hankali kan sana'o'i da kasuwanci da fatauci na gargajiya da kuma yadda zamani ya sauya su. Babi na uku ya gabatar da tarihin intanet, ma'anarsa, bunƙasarsa, da tasirinsa ga Hausawa da kuma tasirin Hausawa a kan intanet. Babi na huɗu ya duba hanyoyin neman kuɗi a kan intanet, kamar ayyukan ƙwadago, tallace-tallace, dillanci, da sauran ayyukan fasaha da kimiyyar harshe. Babi na biyar ya bayyana hanyoyin tanadi ta intanet, ciki har da adana kuɗi a bankuna, lalitocin kan intaent, da kadarorin intanet. A ƙarshe, babi na shida ya kawo matakan naƙaltar biɗa da tanadi a kan intanet, abubuwan da ake buƙata don samun nasara (kamar ilimin kwamfuta da ƙwarewa), da tagomashi da ƙalubalen da suke tattare da wannan harkar. A taƙaice, littafin ya nuna cewa intanet wata dama ce mai girma ga Hausawa, amma tana buƙatar shiri da ƙwarewa don cin nasara a cikinta.