Logo Lanfrica

Kasuwanci a Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21

Domaine:

natural language processingdigital infrastructure

Type de record:

paper
Créateur:
SanYanBab
Éditeur:
Yob
Hôte:avatar
Sannu a hankali al’ummun duniya na ƙara rungumar kasuwancin duniyar intanet. Ciki har da Hausawa. Wannan ne babban dalilin gudanar da binciken inda aka nazarci nau’uka da yanaye-yanayen kasuwancin kan intanet da alfanu da ƙalubalen da ke tare da su da kuma hanyoyin fuskantar waɗannan ƙalubale. Manyan dabarun da aka yi amfani da su wajen tattaraa bayanai su ne nazartar bayanan kan intanet kai tsaye da kuma hira da Hausawan da abin ya shafa. An ɗora aikin a kan ra’in Pulatoriyya (Platonism) inda aka kalli kasuwancin duniyar intanet a matsayin mai cin gashin kansa daga kasuwancin duniyar zahiri (duk da cuɗanyar da suke yi da juna a waɗansu lokuta). Binciken ya gano nau’ukan kasuwancin intanet guda biyar da Hausawa ke gudanarwa. A ɓangare guda kuwa, binciken ya gano cewa, kasuwancin kan intanet ya kasance cigaba duk da waɗansu ƙalubale da ya ƙunsa. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da sa hannun gwamnatoci da hukumomi da ɗaiɗaikun mutane domin bin matakai da amfani da dabarun kauce wa gurɓata muhalli da yanayi yayin gudanar da hada-hadar kasuwanci a duniyar intanet.