Logo Lanfrica

Hoton Waibuwar Hausawa a Cikin Waƙoƙin Dakta Mamman Shata

Domaine:

natural language processing
Créateur:
GobSan
Éditeur:
Uma
Hôte:avatar
Masana da manazarta sun tafi kan cewa, daga cikin adabin al’umma (na baka ko rubutacce), mutum na iya fahimtar salon rayuwar al’ummar na gaba ɗaya. Wannan ya haɗa da tunaninsu da imaninsu da fahimtarsu da al’adunsu da tsarin zamantakewa da dai sauransu. Da ma dai an ba da ma’anar adabi da: “Madubi ko hoton duba rayuwar al’umma.” A ɓangare guda kuwa, waƙa na ɗaya daga cikin manyan rukunnen adabi da ke taka muhimmiyar rawa tare da yin gagarumin tasiri a kan al’amuran rayuwar al’umma na yau da kullum. Wannan ya haɗa da siyasarsu da addininsu da iliminsu da ma sauran abubuwan da suka shafi al’ada. Mawaƙa na taka muhimmiyar rawa wurin fito da tunanin al’umma. A bisa wannan zaren tunani ne takardar ta ginu, inda take ƙoƙarin hango waibuwar Hausawa daga bakin Dakta Mamman Shata. Shata yakan danganta mutum da aljani ko kuma ya ba shi wata siffa ko ɗabi’a ta aljani domin nuna shahara da buwayar mutumin. Haka ma yakan danganta magani da aljani a wasu daga cikin waƙoƙinsa. Wannan takarda ta bibiyi irin waɗannan waƙoƙi da suka haɗa da ‘Malam Babba na Ƙofar Gabas,’ da ‘Hasan Sarkin Dogarai,’ da ‘Mamman Sakwkato Kyaftin,’ da kuma ‘Waƙar Sarkin Bori Sule.’ Daga ƙarshe takardar ta fahimci cewa, Bahaushe ya yarda da wanzuwar aljani har ma ya ɗauke shi a matsayin halitta mai matuƙar hatsabibanci. Bugu da ƙari, Bahaushe na danganta magani da aljani. A taƙaice, Bahaushe ya tafi kan cewa, ƙololuwar buwaya kan samu ga ɗan Adam yayin da ya yi cuɗanya da aljani.