Logo Lanfrica

Jirwayen Kishi a Wasu Waƙoƙin Baka Na Mata

Domaine:

natural language processing

Type de record:

paper
Créateur:
BakSan
Éditeur:
Dep
Hôte:avatar
Manufar wannan takarda ita ce fito da hoton ɗabi’ar kishi a wurin matan Hausawa. An yi garkuwa da wasu waƙoƙin baka na musamman da suke gudanarwa domin ganin wannan hoto na kishi. Kadadar nazarin ta taƙaita ga laluben kishin da ya bayyana a waƙoƙin da suke gudanarwa a lokutan wasu al’adu kamar na daɓe da raino da kuma gaɗa. An yi haka ne domin fayyace yadda kishi yake a rayuwarsu da kuma a yanayin zamantakewarsu. Takardar ta yi amfani da hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da hira da sauraren waƙoƙi daga bakin wasu daga cikin matan da suke rera su. Haka kuma, an dubi wasu daga cikin ayyukan da magabata suka gudanar a matakan ilimi daban-daban domin a naƙalci batun da ake nazari, sannan kuma a cike giɓin da ake da shi a wannan fage. Binciken ya gano cewa, akwai nason kishi a cikin wannan ɓangaren adabin baka. Bugu da ƙari, tasirin da kishi yake da shi a wurin mata, shi ne ya sa ya shiga cikin waƙoƙin da suke gudanarwa na musamman. Daga ƙarshe, takardar ta ba da shawara ga jami’o’i da hukumomin adana tarihi da al’adu da masana a kan su bayar da cikakkiyar kulawar da ta kamata don ganin an zurfafa bincike wajen gano ɓirɓishin kishi a sauran ɓangarorin adabin Hausa.