Logo Lanfrica
  • Accueil
  • Atlas
  • Analyses
  • Documentation
  • Sign in

© 2026 Lanfrica. Tous droits réservés. Tous les droits d'auteur des ressources affichées sur le site Web Lanfrica appartiennent aux détenteurs de droits d'auteur d'origine, sauf indication contraire explicite.

Wasannin Kwaikwayo Na Hausawa

Créateur:
GobSan
Éditeur:
WT
Hôte:avatar
Haƙiƙa, wasannin kwaikwayo na gargajiya sun kasance wani ɓangare na rayuwar ɗan’adam. Wannan kuwa bai tsaya a kan Hausawa ba kawai, ya shafi dukkanin al’ummun duniya da ke ƙasashe daban-daban. Sai dai akan sami bambance-bambancen salo da siga na waɗannan wasanni, wanda hakan ya danganta ga al’ada da yanayin wurin zama na masu wannan wasa. Wasannin kwaikwayon da Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni na fuskantar dusashewa, tamkar dai sauran al’adun Hausawan. Wannan na faruwa ne sakamakon dalilai masu dama waɗanda za a iya taƙaita su da furucin tasirin zamani. Lura da wannan ƙoƙarin ɓacewa da mafi yawan wasannin kwaikwayo na gargajiya ke yi, akwai buƙatar killace su wuri ɗaya a matsayin wani kundin da zai kasance abin waiwaiya a kodayaushe. Yin hakan zai sanya ko da wasannin kwaikwayon sun gushe a zamani, za su kasance a killace har Madi. Marubutan wannan Littafin sun tattara wasannin gargajiya na Hausawa guda ɗari biyu da goma shahuɗu (214) a shekara ta 2021. Sun wallafa su a cikin littafi mai suna Wasanni a Ƙasar Hausa. Littafin ya ƙunshi dukkannin nau’ukan wasanni – na kwaikwayo da waɗanda ba na kwaikwayo ba. Daga baya ne suka yi tunanin ware wasannin kwaikwayo daga cikinsu. An yi nasarar ware wasannin kwaikwayo guda 50. An raba littafin zuwa babuka shida (6). Babi na farko yana ɗauke da gabatarwa. A ciki an kawo bayani game da ma’anar wasan kwaikwayo. An kuma kawo amfanin wasannin kwaikwayo da rabe-rabensu. Babi na biyu zuwa na biyar kuwa na ƙunshe da bayanai game da wasannin kwaikwayo na gargajiya daban-daban. Sun haɗa da na yara maza da yara mata da na tarayya. A gefe guda kuwa, an kawo na manya maza da mata. Babi na shida wanda shi ne na ƙarshe, yana ƙunshe da bayani game da tasirin zamani a kan wasannin kwaikwayon Bahaushe na gargajiya. Bayan an kawo jerin manazarta, sai kuma aka biyo baya da ratayen waɗannan wasannin kwaikwayo na gargajiya cikin tsararren jadawali. An yi hakan ne domin samar da haske ga mai karatu ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci a kan kowane wasa kai tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa da suka haɗa da: i. Sunan wasa ii. Masu wasa iii. Rukunin wasa iv. Kayan aiki v. Amfanin wasa

Visit

doi.orgzenodo.org

Languages

Gbaya, NorthwestHausaKaanKomaMaasaiManyaMbayNyankpaTeke-TsaayiTupuri+2

Licenses

Creative Commons Attribution 4.0 Internationalhttps://creativecommons.org/licenses/by/4.0/legalcode

Similaires

Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na MutuwaKamancin Jinsi a Sunayen Yanka na Hausawa da Wasu Harsuna (Larabci da Ingilishi)ZAMANI RIGA: BUKIN SAUKAR ALQUR'ANI A TSAKANIN AL'UMMAR HAUSAWA A QARNI NA 21Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu)Tasirin Finafinai a Kan Al'adun Hausawa: Keɓaɓɓen Nazari a Kan Wasu Ɗabi'u Na Musamman a Cikin Fina-Finan HausaZamantakewar Hausawa Jiya da Yau

Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na Mutuwa

Manufar wannan bincike ita ce nazarin ƙwaƙƙwafi domin gano nau’ukan tasirin da addinin Musulunci ya

Kamancin Jinsi a Sunayen Yanka na Hausawa da Wasu Harsuna (Larabci da Ingilishi)

Daga cikin hanyoyi masu yawa da masana da manazarta suka danganta al’ummar Hausawa da Larabawa, akwa

ZAMANI RIGA: BUKIN SAUKAR ALQUR'ANI A TSAKANIN AL'UMMAR HAUSAWA A QARNI NA 21

Tsakure Wannan takarda ta tattuna irin sauye-sauyen da zamani ya kawo a al’adar bukin saukar Alqur’

Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu)

The focal point of "Sunayen Hausawa" (The Hausa Names) is an in-depth exploration of the names and n

Tasirin Finafinai a Kan Al'adun Hausawa: Keɓaɓɓen Nazari a Kan Wasu Ɗabi'u Na Musamman a Cikin Fina-Finan Hausa

An daɗe ana amfani da wasannin kwaikwayo wajen isar da saƙwanni ga al’ummar Hausawa. Saƙwannin sun s

Zamantakewar Hausawa Jiya da Yau

Hausawa kan ce wanda ya tuna bara bai ji daɗin bana ba. Haƙiƙa zamantakewar Hausawa a da ta kasance